4 Sa'an nan ya gina Tadmor a jeji, a Hamat kuwa ya gina biranen ajiya.
4 Ya kuma gina Tadmor a hamada da kuma dukan biranen ajiyar da ya gina a Hamat.
Suka kuwa naɗa musu shugabannin aikin gandu domin su wahalshe su da mawuyacin aiki. Aka sa su su gina wa Fir'auna biranen ajiya, wato Fitom da Ramases.
Sa'ad da Toyi Sarkin Hamat ya ji labari Dawuda ya ci dukan rundunar Hadadezer da yaƙi,
Sai Sulemanu ya tafi ya ci Hamat-zoba da yaƙi.
Ya kuma gina Bet-horon ta kan tudu da Bet-horon ta kwari, birane masu kagara kuwa ya gina musu garu, da ƙofofi, da ƙyamare,
Yehoshafat ya daɗa ƙasaita, ya giggina kagarai, da biranen ajiya a Yahuza.