Dawuda kuma ya ci Hadadezer ɗan Rehob, Sarkin Zoba, da yaƙi lokacin da shi Hadadezer yake kan tafiya zuwa Kogin Yufiretis don ya tabbatar da ikonsa a wurin.
Sauran ayyukan Yerobowam na biyu, da dukan abin da ya yi, da ƙarfinsa, da yaƙi da ya yi, da yadda ya ƙwato wa Isra'ila Dimashƙu da Hamat waɗanda suke na Yahuza, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.