“Muka yi gaba, muka bar zuriyar Isuwa 'yan'uwan nan namu waɗanda suke zaune a ƙasar tuddai ta Seyir, muka bar hanyar Araba, da hanyar Elat da Eziyon-geber. Muka juya, muka nufi wajen jejin Mowab.
Haka Sulemanu ya kammala aikinsa, da aka aza harsashin gina Haikalin Ubangiji, har zuwa ran da aka gama. Haka kuwa aka kammala aikin Haikalin Ubangiji.