Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Tarihi 7:9 - Littafi Mai Tsarki

9 A rana ta takwas kuwa suka yi wani muhimmin taro, domin su keɓe bagaden. Sun yi kwana bakwai suna yin bikin.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 A rana ta takwas sai suka yi taro, gama sun yi bikin keɓewar bagade na kwana bakwai da kuma biki na ƙarin kwana bakwai.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Tarihi 7:9
10 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A kwana bakwai ɗin za su riƙa miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. A rana ta takwas kuma sai su yi muhimmin taro na sujada, su miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. Rana ce ta yin sujada, kada su yi aiki.


Ku sa a yi azumi, Ku kira muhimmin taro. Ku tara dattawa da dukan mutanen ƙasar A Haikalin Ubangiji Allahnku, Ku yi kuka ga Ubangiji.


Kowace rana, tun daga rana ta fari zuwa rana ta ƙarshe, Ezra yakan karanta musu daga cikin littafin dokokin Allah. Suka kiyaye idin har kwana bakwai. A rana ta takwas kuma suka muhimmin taro bisa ga ka'ida.


Sai dukan taron suka yarda su ci gaba da yin idin har waɗansu kwana bakwai ɗin kuma, sai suka ci gaba da yin idin har kwana bakwai da murna.


Sa'an nan kuma Sulemanu ya yi biki na kwana bakwai, shi da dukan jama'ar Isra'ila. Mutane suka zo, tun daga Mashigin Hamat a arewa, har zuwa iyakar ƙasar Masar a kudu, suka hallara a gaban Ubangiji Allahnmu.


Kwana shida za ku yi kuna cin abinci marar yisti, amma a rana ta bakwai sai ku yi muhimmin taro saboda Ubangiji Allahnku. Kada ku yi aiki a wannan rana.


Sai shugabanni suka miƙa hadayu domin keɓewar bagade a ranar da aka zuba masa mai. Suka fara miƙa sadakokinsu a bagaden,


A ran ashirin da uku ga watan bakwai, sai sarki ya sallami jama'a su koma gidajensu, suna ta murna da farin ciki a zuciyarsu saboda alherin da Ubangiji ya nuna wa Dawuda, da Sulemanu, da kuma jama'arsa Isra'ila.


Kwana bakwai za ka ɗauka na yin kafara don bagaden, ka keɓe shi, haka kuwa bagaden zai zama mafi tsarki. Duk abin da ya taɓa bagaden zai tsarkaka.”


Dukan jama'ar Isra'ila suka taru gaban sarki Sulemanu, wurin biki a watan Etanim, wato wata na bakwai.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ