2 Tarihi 7:6 - Littafi Mai Tsarki6 Sai firistoci suka tsaya a matsayinsu, haka kuma Lawiyawa suka tsaya a nasu matsayi riƙe da kayansu na bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe, waɗanda sarki Dawuda ya yi domin yabon Ubangiji, gama madawwamiyar ƙaunarsa tabbatacciya ce har abada. A duk lokacin da Dawuda zai yabi Ubangiji tare da su, sai firistoci waɗanda suke daura da su su busa ƙaho, sa'an nan sai dukan Isra'ilawa su miƙe tsaye. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20206 Firistoci suka ɗauki matsayinsu, haka kuma Lawiyawa suka tsaya a matsayinsu riƙe da kayansu na bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe na Ubangiji, waɗanda Sarki Dawuda ya yi domin yabon Ubangiji. An yi amfani da su sa’ad da ake godiya, ana kuma cewa, “Ƙaunarsa dawwammamiya ce har abada.” Kurkusa da Lawiyawa, firistoci suka busa ƙahoninsu, dukan Isra’ila kuwa suna a tsaye. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ya zama aikin mabusan ƙaho ne, da mawaƙa duka, su haɗa kai, har a ji su suna yabon Ubangiji, suna godiya, sa'ad da suka ɗaga waƙa daidai da muryar ƙaho da ta kuge, da dukan kayan bushe-bushe suka yi ta raira waƙa cewa, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji Gama shi nagari ne, Ƙaunarsa kuwa madawwamiya ce.” Gidan kuwa, wato Haikalin Ubangiji, ya cika da girgije,