Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Tarihi 7:19 - Littafi Mai Tsarki

19 Amma idan ka juya, ka bar dokokina da umarnaina waɗanda na sa a gabanka, har ka shiga bautar gumaka kana musu sujada,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 “Amma in ka juya daga gare ni ka yashe ƙa’idodi da umarnan da na ba ka, ka yi gaban kanka don ka bauta wa waɗansu alloli ka kuma yi musu sujada,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Tarihi 7:19
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Amma idan ba za ku yi biyayya da Ubangiji Allahnku ba, ko kuwa ba ku lura kuka aikata umarnansa da dokokinsa waɗanda nake umartar da su yau ba, to, dukan waɗannan la'ana za su auko muku, su same ku.


“Amma idan ba za ku kasa kunne gare ni ba, to, za ku sha hukunci.


“Kai kuwa ɗana Sulemanu, sai ka san Allah na tsohonka, ka bauta masa da zuciya ɗaya, da kuma yardar rai, gama Ubangiji mai binciken dukan zukata ne, ya kuma san kowane irin nufi da tunani. Idan ka neme shi, za ka same shi, in kuwa ka rabu da shi, shi ma zai yi watsi da kai har abada.


Amma idan kuka ci gaba da aikata mugunta, za a shafe ku, ku da sarkinku.”


Gama idan kun ƙi binsa, zai sāke yashe ku a jeji. Ku ne kuwa za ku zama sanadin hallakar mutanen nan duka.”


Sai Ubangiji ya ce, “Saboda sun bar dokata wadda na sa a gabansu, ba su yi biyayya da maganata ko su yi aiki da ita ba.


Kada ka rusuna musu, kada kuwa ka bauta musu, gama ni Ubangiji Allahnka, mai kishi ne. Nakan hukunta 'ya'ya har tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suke ƙina.


domin kada ku yi cuɗanya da sauran al'umman da take zaune tare da ku, kada ku ambaci sunayen gumakansu, ko ku rantse da su, ko ku bauta musu, ko ku sunkuya musu.


Ba zan ƙara fitar da Isra'ila daga ƙasar da na ba kakanninku ba, in dai sun lura, sun kiyaye, sun aikata dukan abin da na umarce su, da dukan shari'a, da dokoki, da ka'idodi da aka bayar ta hannun Musa.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ