Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Tarihi 7:16 - Littafi Mai Tsarki

16 Yanzu fa na riga na zaɓi wannan Haikali, na kuwa keɓe shi domin sunana ya kasance a wurin har abada. Idanuna da zuciyata kuma za su kasance a wurin kullayaumin.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 Na zaɓi na kuma tsarkake wannan haikali saboda Sunana yă kasance a can har abada. Idanuna da kuma zuciyata kullum za su kasance a can.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Tarihi 7:16
22 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Yanzu idanuna za su kasance a buɗe, kunnuwana kuma za su saurari addu'ar da za a yi a wannan wuri.


Sa'an nan Ubangiji ya bayyana ga Sulemanu da dare, ya ce masa, “Na ji addu'arka, na kuwa zaɓi wannan wuri domin kaina, domin ya zama Haikalin miƙa hadaya.


Ubangiji ya ce masa, “Na ji addu'arka da roƙe-rokenka da ka yi a gare ni, saboda haka na tsarkake Haikalin nan da ka gina, na kuma sa sunana ya kasance a wurin har abada. Idanuna da zuciyata kuma za su kasance a wurin kullum.


Ka dubi wajen Haikalin nan dare da rana, wurin da ka yi alkawari za ka sa sunanka, ka kasa kunne ga addu'ar da bawanka zai yi wajen wannan wuri,


Domin a cikinsa ne cikin jiki dukkan cikar Allahntaka take tabbata.


Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Ubangiji ya tsauta maka, kai Shaiɗan! Ubangiji wanda ya zaɓi Urushalima ya tsauta maka. Ai, wannan mutum kamar itace ne wanda aka fizge daga cikin wuta.”


“A nan zan zauna har abada. A nan kuma nake so in yi mulki.


Sai aka ji wata murya daga Sama ta ce, “Wannan shi ne Ɗana ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi ƙwarai.”


Ya gina bagadai a Haikalin Ubangiji inda Ubangiji ya ce, “A Urushalima zan sa sunana.”


Idan sun komo gare ka da zuciya ɗaya, da dukan ransu a ƙasar abokan gabansu waɗanda suka kai su bauta, suka yi addu'a gare ka, suna fuskantar ƙasarsu wadda ka ba kakanninsu, da birnin da ka zaɓa, da Haikalin da na gina saboda sunanka,


“Idan jama'arka sun tafi su yi yaƙi da abokan gābansu, idan sun yi addu'a a gare ka, suna fuskantar birnin nan da ka zaɓa, da Haikalin nan wanda na gina saboda sunanka,


“Idan an hore su da rashin ruwan sama, saboda sun yi maka zunubi, idan sun tuba, suna fuskantar wannan Haikali, suka yi addu'a, suka kuma yabe ka,


‘Tun daga ran da na fito da mutanena Isra'ila, daga Masar, ban zaɓi wani birni daga cikin kabilan Isra'ila inda zan gina Haikali domin sunana ba, amma na zaɓi Dawuda ya shugabanci mutanena Isra'ilawa.’ ”


Sai ku yi murna a gaban Ubangiji Allahnku a inda Ubangiji Allahnku ya zaɓa don ya tabbatar da sunansa, ku da 'ya'yanku mata da maza, da barorinku mata da maza, da Balawen da suke zaune a garinku, da baƙo, da maraya, da gwauruwa ta gaske, waɗanda suke zaune tare da ku.


Idan wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa don ya sa sunansa ya yi muku nisa ƙwarai, to, sai ku yanka daga cikin garken shanunku, ko daga tumaki da awaki, waɗanda Ubangiji ya ba ku, kamar yadda na umarce ku. Za ku iya ci yadda kuke bukata a garuruwanku.


Amma kai, idan za ka yi zamanka a gabana kamar yadda tsohonka Dawuda ya yi, ka kuma aikata bisa ga dukan abin da na umarce ka, ka kiyaye dokokina da farillaina,


Kada ku yi taurin kai kamar yadda kakanninku suka yi, amma ku miƙa kanku ga Ubangiji, ku zo Wuri Mai Tsarki, wanda ya tsarkake har abada, ku bauta wa Ubangiji Allahnku, domin ya huce daga zafin fushin da yake yi da ku.


Ubangiji ya yaɓi Sihiyona, A can yake so ya gina Haikalinsa, ya ce,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ