Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Tarihi 7:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Sa'ad da Sulemanu ya gama yin addu'arsa, sai wuta ta sauko daga sama, ta cinye hadayar ƙonawa tare da sauran hadayu, darajar Ubangiji kuma ta cika Haikalin.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Sa’ad da Solomon ya gama yin addu’a, sai wuta ya sauko daga sama ya cinye hadaya ta ƙonawa da kuma sadakokin, ɗaukakar Ubangiji kuwa ta cika haikalin.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Tarihi 7:1
26 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ubangiji kuwa ya sa wuta ta faɗo, ta cinye hadaya ta ƙonawa, da itacen, da duwatsun, da ƙurar, ta kuma lashe ruwan da yake cikin wuriyar.


Dawuda ya gina wa Ubangiji bagade a wurin, ya miƙa hadayu na ƙonawa da hadayu na salama. Sai ya yi roƙo ga Ubangiji, Ubangiji kuwa ya amsa masa ta wurin wutar da ta sauko daga sama a bisa bagaden hadayar ta ƙonawa.


Za ku yi kira ga sunan Ba'al naku, ni kuma zan kira ga sunan Ubangiji. Allahn da ya amsa da wuta, shi ne Allah.” Jama'a duka suka yi sowar nuna yarda da wannan.


Sa'an nan ya kawo ni a gaban haikalin ta hanyar ƙofar arewa. Da na duba, na ga zatin Ubangiji cike da Haikalin, sai na faɗi rubda ciki.


Ruhu kuwa ya ɗaga ni, ya kai ni a farfajiya ta can ciki, sai ga zatin Ubangiji ya cika Haikali.


Sa'ad da rana ta fāɗi aka kuwa yi duhu, sai ga tanderun wuta mai hayaƙi da jiniya mai harshen wuta suka ratsa tsakanin abubuwan nan da aka tsattsaga a tsaka.


Mala'ikan Ubangiji kuwa ya miƙa kan sandan da yake hannunsa, ya taɓa naman da wainar, sai wuta ta fito daga dutsen ta cinye naman da wainar. Mala'ikan Ubangiji kuwa ya ɓace masa.


Birnin kuwa ba ya bukatar rana ko wata su haskaka shi, domin ɗaukakar Allah ita ce haskensa, Ɗan Ragon kuma fitilarsa.


Bayan sun yi addu'a, wurin da suke a tattare ya raurawa. Sai duk aka cika su da Ruhu Mai Tsarki, suka yi ta faɗar maganar Allah gabagaɗi.


Sa'ad da nake ta addu'a, ina faɗar zunubina, da na jama'ata Isra'ila, ina kawo roƙe-roƙena wurin Ubangiji Allahna saboda tsattsarkan tudun Allahna.


Zan amsa addu'o'insu tun ma kafin su gama yin addu'a gare ni.


Nan ne zan sadu da Isra'ilawa in tsarkake wurin da ɗaukakata.


Ga shi, hayaƙi ya tunnuƙe dutsen Sina'i duka, saboda Ubangiji ya sauko a bisa dutsen da wuta. Hayaƙi kuwa ya tunnuƙe, ya yi sama kamar na wurin narka ma'adinai, dutsen duka ya girgiza ƙwarai.


Sa'an nan kuma Ubangiji zai yarda da hadayun mutanen Yahuza da na Urushalima kamar yadda yake a zamanin dā.


Da Sulemanu ya gama ginin Haikalin Ubangiji da na fāda, da dukan abin da ya so ya yi,


Ya Ubangiji, ina ƙaunar Haikali inda zatinka yake, Inda ɗaukakarka yake zaune.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ