Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Tarihi 6:30 - Littafi Mai Tsarki

30 sa'an nan za ka ji daga wurin zamanka a Sama, ka yi gafara, ka kuwa sāka wa kowa bisa ga al'amuransa, wanda ka san zuciyarsa, gama kai kaɗai ne ka san zukatan mutane,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

30 sai ka ji daga sama, mazauninka. Ka gafarta, ka kuma yi da kowane mutum gwargwadon duk abin da yake yi, da yake ka san zuciyarsa (gama kai kaɗai ka san zukatan mutane),

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Tarihi 6:30
18 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Kai kuwa ɗana Sulemanu, sai ka san Allah na tsohonka, ka bauta masa da zuciya ɗaya, da kuma yardar rai, gama Ubangiji mai binciken dukan zukata ne, ya kuma san kowane irin nufi da tunani. Idan ka neme shi, za ka same shi, in kuwa ka rabu da shi, shi ma zai yi watsi da kai har abada.


Amma Ubangiji ya ce masa, “Kada ka kula da kyan tsarinsa, ko tsayinsa, domin ba shi nake so ba, gama yadda Ubangiji yake gani, ba haka mutum yake gani ba. Mutum yakan dubi kyan tsari ne kawai, amma Ubangiji yakan dubi zuciya.”


Zan kashe 'ya'yanta tashi ɗaya, dukan ikilisiyoyi kuma za su sani Ni ne mai fayyace birnin zuciya. Zan kuma saka wa kowannenku gwargwadon aikinsa.


Ba wata halittar da za ta iya ɓuyar masa, amma kowane abu a fili yake, a shanye sosai a gaban idon wannan da za mu ba da lissafi a gabansa.


domin ya san zuciyar kowa, ba kuma sai wani ya shaidi mutum a wurinsa ba, domin shi kansa ya san abin da yake zuciyar ɗan adam.


Domin Ɗan Mutum zai zo da ɗaukakar Ubansa tare da mala'ikunsa. A sa'an nan ne zai sāka wa kowane mutum gwargwadon aikinsa.


“Domin haka ni Ubangiji Allah zan hukunta ku, ku mutanen Isra'ila, kowa gwargwadon ayyukansa. Ku tuba, ku bar laifofinku domin kada su zama muku dalilin halaka.


Ni Ubangiji nakan bincike tunani, In gwada zuciya, Domin in sāka wa kowane mutum gwargwadon al'amuransa, Da kuma gwargwadon ayyukansa.


Madawwamiyar ƙauna, ta Ubangiji ce. Kai kanka, ya Ubangiji, kake sāka wa Kowane mutum bisa ga ayyukansa.


sai ka ji addu'arsa. Ka kasa kunne gare shi, a wurin zamanka a Sama, ka gafarta masa. Kai kaɗai ka san tunanin dukan mutane. Ka yi da kowa bisa ga abin da ya yi,


Da yake na sani, ya Allahna, kakan gwada zuciya, kana ƙaunar gaskiya, bisa ga amincewar zuciyata, da yardar rai, na miƙa maka dukan waɗannan abubuwa. Ina murna da ganin jama'arka waɗanda suke nan a tattare, sun kawo maka sadakokinsu da yardar rai.


kowace irin addu'a, kowane irin roƙo da kowane mutum, ko jama'ar Isra'ila suka yi, ko wannensu yana sane da irin wahalarsa, da baƙin cikinsa, ya kuwa ɗaga hannunsa wajen wannan Haikali,


don su yi tsoronka su yi tafiya bisa ga dokokinka muddin ransu, a ƙasar da ka ba kakanninmu.


Ko lahira ba za ta hana Ubangiji ya san abin da yake can ba. Ƙaƙa fa mutum zai iya ɓoye wa Allah tunaninsa?


Ka kuma ba ɗana Sulemanu cikakkiyar zuciya, har da zai kiyaye umarnanka, da shaidunka, da dokokinka, domin ya aikata su duka, ya kuma gina Haikali wanda na riga na yi tanadi dominsa.”


Allah ne mai kiyaye ni, Yakan ceci waɗanda suke yi masa biyayya.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ