Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Tarihi 6:23 - Littafi Mai Tsarki

23 sai ka ji ka yi wa bayinka shari'a daga Sama, ka hukunta wa mugun, ka ɗora masa alhakinsa, ka baratar da adalin, ka ba shi sakayyar adalcinsa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

23 sai ka ji daga sama ka kuma yi wani abu. Ka shari’anta tsakanin bayinka, kana sāka wa mai laifi ta wurin kawo a kansa hakkin abin da ya yi. Ka nuna cewa marar laifi ba shi da laifi, ta haka a fiffita rashin laifinsa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Tarihi 6:23
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Wanda ya yi zunubi shi zai mutu. Ɗa ba zai ɗauki hakkin laifin mahaifinsa ba, mahaifi kuma ba zai ɗauki hakkin laifin ɗansa ba. Adalcin adali nasa ne, muguntar mugu kuma tasa ce.


Gama mai hallakarwa ya auka wa Babila, An kama sojojinta, An kuma kakkarya bakunansu, Gama Ubangiji shi Allah ne, mai sakayya, Zai yi sakayya sosai.


Da wanda ya baratar da mugun da wanda ya kā da adali, duk abin ƙi suke ga Ubangiji.


Saboda haka za ku karɓi sakayyarku, ayyukanku za su cuce ku.


Amma kana gani, kana kuma lura da masu shan wuya, da masu ɓacin rai, Koyaushe kuma a shirye kake ka yi taimako. Mutum wanda ba shi da mai taimako yakan danka kansa gare ka, Gama kullum kakan taimaki masu bukata.


‘Hakika, kamar yadda jiya na ga jinin Nabot da na 'ya'yansa, ni Ubangiji, zan sāka maka saboda wannan gona.’ Yanzu sai ka ɗauke shi, ka jefar da shi a wannan gona kamar yadda Ubangiji ya faɗa.”


“Idan wata gardama ta tashi tsakanin mutane, suka je gaban shari'a, alƙalai kuwa suka yanke musu maganar, suka kuɓutar da marar laifi, suka kā da mai laifin,


Bayan da ya sa ta ta sha ruwan, idan ta ƙazantar da kanta, ta kuwa ci amanar mijinta, ruwan nan mai kawo la'ana zai shiga cikinta ya zama la'ana mai ɗaci, cikinta zai kumbure, cinyarta ta shanye, matar kuwa za ta zama la'ananniya cikin jama'arta.


Waɗanda suke masu sonkai, da waɗanda suke ƙin bin gaskiya, da masu bin rashin adalci, zai saka musu da fushi da hasala.


“Idan wani ya yi wa maƙwabcinsa laifi, har aka sa shi ya rantse, ya kuwa zo ya rantse a gaban bagaden a wannan Haikali,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ