Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Tarihi 6:17 - Littafi Mai Tsarki

17 Saboda haka, ya Ubangiji, Allah na Isra'ila, ka tabbatar da maganarka wadda ka yi wa bawanka Dawuda.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

17 Yanzu kuwa, ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, bari maganarka da ka yi alkawarta wa bawanka Dawuda yă cika.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Tarihi 6:17
10 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sa'an nan zan cika maganar rantsuwa da na rantse wa kakanninku, da na ce zan ba su ƙasa wadda take cike da albarka kamar yadda yake a yau.’ ” Irmiya ya ce, “Amin, amin, ya Ubangiji.”


Zan ba ka dukiya daga cikin duhu, a asirtattun wurare, Sa'an nan za ka sani ni ne Ubangiji, Allah na Isra'ila kuma, shi ne ya zaɓe ka.


“Sa'ad da jama'ata ta bukaci ruwa, Sa'ad da maƙogwaronsu ya bushe da ƙishi, Sa'an nan ni Ubangiji, zan amsa addu'arsu, Ni Allah na Isra'ila, ba zan taɓa yashe su ba.


ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na Isra'ila, ba wani Allah kamarka a sama ko a duniya, wanda yake cika alkawari, kana nuna madawwamiyar ƙauna ga bayinka masu tafiya a gabanka da zuciya ɗaya.


Sai ya ce, “Ubangiji Maɗaukaki ne, Allah na Isra'ila wanda ya yi wa tsohona Dawuda alkawari, ga shi kuwa ya cika shi, gama ya ce,


Suka ga Allah na Isra'ila. Wurin da yake ƙarƙashin tafin ƙafafunsa yana kama da daɓen da aka yi da dutsen yakutu, garau kamar sararin sama.


Manowa fa ya tashi ya tafi tare da ita. Da ya zo wurin mutumin, sai ya tambaye shi, “Kai ne mutumin da ya yi magana da macen nan?” Sai ya amsa ya ce, “Ni ne.”


Yanzu fa, ya Ubangiji, Allah na Isra'ila, ka cika alkawarin da ka yi wa bawanka tsohona cewa, ‘Daɗai, ba za a rasa wanda zai hau gadon sarautar Isra'ila ba, in dai 'ya'yanka maza za su lura da al'amuransu, don su yi tafiya bisa ga shari'ata, yadda kai ka yi tafiya a gabana.’


“Ashe kuwa Allah zai zauna tare da ɗan adam a duniya? Ga shi kuwa, sama da saman sammai ba su iya ɗaukarka ba, balle fa ɗakin da na gina.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ