Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Tarihi 6:13 - Littafi Mai Tsarki

13 Sulemanu ya riga ya yi dakali na tagulla, tsawonsa kamu biyar, fāɗinsa kamu biyar, tsayinsa kamu uku, ya ajiye shi a tsakiyar filin, ya tsaya a kai. Ya durƙusa a gwiwoyinsa, a idon dukan taron jama'ar Isra'ila, ya ɗaga hannuwansa sama,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 Dā ma ya riga ya gina dakalin tagulla, mai tsawo kamu biyar, fāɗi kamu biyar da kuma tsayi kamu uku, ya kuma sa shi a tsakiyar filin waje. Ya tsaya a kan dakalin ya kuma durƙusa a gaban dukan taron Isra’ila ya buɗe hannuwansa sama.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Tarihi 6:13
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Da Sulemanu ya gama wannan addu'a da roƙo ga Ubangiji, sai ya tashi daga gaban bagaden Ubangiji, inda yake a durƙushe da hannuwansa a miƙe zuwa sama.


Sai Ezra, magatakarda, ya tsaya a wani dakali na itace, wanda suka shirya musamman domin wannan hidima. Sai Mattitiya, da Shema, da Anaya, da Uriya, da Hilkaya, da Ma'aseya, suka tsaya a wajen damansa, a wajen hagunsa kuwa Fedaiya, da Mishayel, da Malkiya, da Hashum, da Hashbaddana, da Zakariya, da Meshullam suka tsaya.


Ku zo, mu durƙusa, mu yi masa sujada, Mu durƙusa a gaban Ubangiji, Mahaliccinmu!


A lokacin sadakar yamma ɗin, sai na tashi daga yin azumi, da rigata da alkyabbata yagaggu. Na rusuna a gwiwoyina, na ɗaga hannuwana zuwa ga Ubangiji Allahna.


Amma da lokacin tashinmu ya yi, muka tashi muka ci gaba da tafiyarmu, dukansu kuma har da matansu da 'ya'yansu, suka raka mu bayan gari, sa'an nan muka durƙusa a kan gaci, muka yi addu'a, muka yi bankwana da juna.


Da Bulus ya faɗi haka, ya durƙusa, duka suka yi addu'a tare.


Sai ya ɗan rabu da su misalin nisan jifa, ya durƙusa, ya yi addu'a.


Sa'ad da Daniyel ya sani an sa hannu a dokar, sai ya tafi gidansa. Ya buɗe tagogin benensa waɗanda suke fuskantar Urushalima. Sau uku kowace rana yakan durƙusa ya yi addu'a, yana gode wa Allahnsa kamar yadda ya saba.


Sa'an nan ya yi wani shirayi domin firistoci, ya kuma yi wani babban shirayi, ya yi ƙofofi domin shirayun. Ya dalaye ƙyamaren ƙofofin da tagulla.


Babbar farfajiyar fāda, da filin Haikali na ciki da shirayin Haikalin yana da bangaye da jerin katakan al'ul domin kowane jeri uku na yankakkun duwatsu.


Ya gina shirayi na ciki da sassaƙaƙƙun duwatsu jeri uku, da jeri ɗaya na katakan itacen al'ul.


Sulemanu ya miƙe a gaban bagaden Ubangiji a idon dukan taron Isra'ila ya ɗaga hannuwansa.


Musa ya ce masa, “Da fitata daga cikin birnin, zan yi addu'a ga Ubangiji, walƙiya kuwa za ta tsaya, ƙanƙara kuma ta daina, don ku sani duniya ta Ubangiji ce.


Da na ji wannan labari, sai na zauna, na yi kuka. Na yi kwanaki ina baƙin ciki, na yi ta azumi da addu'a a gaban Allah na Sama.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ