Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Tarihi 5:14 - Littafi Mai Tsarki

14 har ma firistoci ba su iya tsayawa su ci gaba da hidima ba saboda girgijen, gama ɗaukakar Ubangiji ta cika Haikalin Allah.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

14 Firistoci ba su iya yin hidimarsu ba saboda girgijen, gama ɗaukakar Ubangiji ta cika haikalin Allah.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Tarihi 5:14
10 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Musa kuwa bai iya shiga alfarwa ta sujada ba domin girgijen yana zaune a bisanta, ɗaukakar Ubangiji kuma ta cika alfarwa.


har firistoci ba su iya tsayawa su gama hidima ba saboda girgijen, gama ɗaukakar Ubangiji ta cika Haikalin Ubangiji.


Firistoci ba su iya shiga Haikalin Ubangiji ba saboda darajar Ubangiji ta cika Haikalin.


Sai Haikalin ya cika da hayaƙi mai fitowa daga ɗaukakar Allah da ikonsa. Ba mai iya shiga Haikalin nan, sai bayan bala'i bakwai na mala'ikun nan bakwai sun ƙare.


Ɗaukakar Ubangiji ta tashi daga kan kerubobin zuwa ƙofar Haikalin. Girgije kuwa ya cika Haikalin, hasken zatin Ubangiji ya cika farfajiyar.


Shi ne kaɗai marar mutuwa, yake kuma zaune a cikin hasken da ba ya kusatuwa. Shi kuwa ba mutumin da ya taɓa ganinsa, ko kuwa zai iya ganinsa. Girma da madawwamin mulki su tabbata a gare shi. Amin, amin.


Nan ne zan sadu da Isra'ilawa in tsarkake wurin da ɗaukakata.


Sa'ad da Sulemanu ya gama yin addu'arsa, sai wuta ta sauko daga sama, ta cinye hadayar ƙonawa tare da sauran hadayu, darajar Ubangiji kuma ta cika Haikalin.


ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na kakanninmu, kai ne Allah na cikin Sama, kai ne kuma kake mulkin dukan al'umman duniya. A gare ka iko da ƙarfi suke, don haka ba wanda ya isa ya jā da kai.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ