2 Tarihi 5:12 - Littafi Mai Tsarki12 Dukan Lawiyawa mawaƙa, wato su Asaf, da Heman, da Yedutun tare da 'ya'yansu maza da 'yan'uwansu, aka sa su su tsaya a gabashin bagade, suna sāye da lilin mai kyau, suna ta kaɗa kuge, da molaye da garayu, ga kuma firistoci ɗari da ashirin masu busa ƙaho tare da su. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202012 Dukan Lawiyawa waɗanda suke mawaƙa, Asaf, Heman, Yedutun da ’ya’yansu maza da dangoginsu, suka tsaya a gefen gabas na bagaden, saye da lilin mai kyau suna kuma kaɗa ganguna, garayu da molaye. Tare da su akwai firistoci 120 masu busan ƙahoni. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sai firistoci suka tsaya a matsayinsu, haka kuma Lawiyawa suka tsaya a nasu matsayi riƙe da kayansu na bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe, waɗanda sarki Dawuda ya yi domin yabon Ubangiji, gama madawwamiyar ƙaunarsa tabbatacciya ce har abada. A duk lokacin da Dawuda zai yabi Ubangiji tare da su, sai firistoci waɗanda suke daura da su su busa ƙaho, sa'an nan sai dukan Isra'ilawa su miƙe tsaye.