2 Tarihi 5:1 - Littafi Mai Tsarki1 Sulemanu ya kammala dukan aikin Haikalin Ubangiji. Sa'an nan ya kawo kayayyakin da tsohonsa Dawuda ya riga ya keɓe, wato azurfa da zinariya, da dukan kayan girke-girke, da tasoshi, ya ajiye su a taskokin Haikalin Allah. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20201 Sa’ad da dukan aikin da Solomon ya yi domin haikalin Ubangiji ya gama, sai ya kawo abubuwan da mahaifinsa Dawuda ya keɓe a ciki, azurfa da zinariya da kuma dukan kayayyaki, ya kuwa sa su a cikin ma’ajin haikalin Allah. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Da wahala mai yawa na yi tanadi domin Haikalin Ubangiji, zinariya wajen talanti dubu ɗari (100,000), da azurfa kuma wajen talanti zambar dubu (1,000,000), domin gina Haikalin Ubangiji. Bayan wannan akwai tagulla da ƙarfe masu tarin yawa. Na kuma tanada katakai da duwatsu. Kai kuma sai ka ƙara a kansu.