Sulemanu ya yi dukan kayayyakin aikin da suke na Haikalin Ubangiji. bagaden zinariya teburin zinariya inda ake ajiye gurasar ajiyewa alkuki na zinariya guda biyar a gefen dama, biyar kuma a gefen hagu a gaban Wuri Mafi Tsarki na can ciki furanni fitilu arautaki finjalai na zinariya hantsuka daruna cokula farantan wuta na zinariya tsantsa almanani na zinariya domin ƙofofin ɗaki na can cikin Haikali, wato Wuri Mafi Tsarki, da ƙofofin Haikalin.