2 Tarihi 4:6 - Littafi Mai Tsarki6 Ya kuma yi daro goma na wanki, ya ajiye biyar a wajen kudu, biyar kuma a wajen arewa, don a riƙa ɗauraye abubuwan da ake hadayar ƙonawa da su. Amma kwatarniya don firistoci su riƙa wanka a ciki ne. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20206 Sa’an nan ya yi daruna goma don wanki ya sa biyar a gefen kudu, biyar kuma a gefen arewa. A cikinsu kayan da za a yi amfani don ɗauraye hadayun ƙonawa, amma firistoci suna amfani da ƙaton kwano mai suna Teku don wanki. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Huram kuma ya yi tukwanen ƙarfe da manyan cokula, da daruna. Haka Huram ya gama dukan aikin da ya yi wa Sulemanu a cikin Haikalin Ubangiji. Ga abin da ya yi. ginshiƙai biyu dajiya da take a kawunan ginshiƙan raga biyu don rufe dajiyar da take a kawunan ginshiƙai siffofin rumman ɗari huɗu domin raga biyu ɗin, da jeri biyu na siffofin rumman domin kowace raga don a rufe dajiyar da take a kawunan ginshiƙan dakalai goma daruna goma a kan dakalan kwatarniya ɗaya siffofin bijimai guda goma sha biyu da kwatarniya take zaune a kai, tukwanen ƙarfe, da manyan cokula, da kwanoni. Dukan kayayyakin aiki a cikin Haikalin Ubangiji waɗanda Huram ya yi wa sarki Sulemanu, an yi su ne da gogaggiyar tagulla.