2 Tarihi 34:9 - Littafi Mai Tsarki9 Sai suka zo wurin Hilkiya babban firist, suka ba shi kuɗin da aka kawo a Haikalin Allah, wanda Lawiyawa, masu tsaron ƙofa, suka tattara daga mutanen Manassa da na Ifraimu, daga sauran Isra'ila, da kuma na dukan Yahuza da Biliyaminu, tare da na mazaunan Urushalima. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20209 Suka tafi wurin Hilkiya babban firist suka ba shi kuɗin da aka kawo cikin haikalin Allah, wanda Lawiyawa masu tsaron ƙofofi sun tattara daga mutanen Manasse, Efraim da dukan raguwar Isra’ila da kuma daga dukan mutanen Yahuda da Benyamin da kuma mazaunan Urushalima. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa'ad da aka gama duka, sai dukan Isra'ilawa da suka hallara, suka bi cikin biranen Yahuza, suka farfashe al'amudan, suka ragargaza Ashtarot, suka farfashe masujadai da bagadai duka da suke a Yahuza da Biliyaminu, da na Ifraimu da Manassa har suka hallakar da su duka. Sa'an nan dukan jama'ar Isra'ila suka koma garuruwansu, ko wanne zuwa mahallinsa.
Sa'an nan sarki Yosiya ya umarci Hilkiya, babban firist, da firistoci masu daraja ta biyu, da masu tsaron ƙofa, su fitar da tasoshin da aka yi wa Ba'al, da Ashtoret, da dukan taurarin sama, daga cikin Haikalin Ubangiji. Sai ya ƙone su a bayan Urushalima a saurar Kidron, sa'an nan ya kwashe tokarsu zuwa Betel.