2 Tarihi 34:3 - Littafi Mai Tsarki3 A shekara ta takwas ta mulkinsa, a lokacin yana yaro, sai ya fara neman Allah na kakansa Dawuda. A shekara ta goma, sha biyu, sai ya fara tsarkake Yahuza da Urushalima daga masujadai, da Ashtarot, da sassaƙaƙƙun siffofi, da siffofi na zubi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20203 A shekara ta takwas ta mulkinsa, yayinda yake matashi, sai ya fara neman Allah na kakansa Dawuda. A shekara ta goma sha biyunsa ya fara tsabtacce Yahuda da Urushalima daga masujadan kan tudu, ginshiƙan Ashera, sassaƙaƙƙun gumaka da kuma siffofin da aka yi zubi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa'an nan sarki Yosiya ya umarci Hilkiya, babban firist, da firistoci masu daraja ta biyu, da masu tsaron ƙofa, su fitar da tasoshin da aka yi wa Ba'al, da Ashtoret, da dukan taurarin sama, daga cikin Haikalin Ubangiji. Sai ya ƙone su a bayan Urushalima a saurar Kidron, sa'an nan ya kwashe tokarsu zuwa Betel.