2 Tarihi 33:3 - Littafi Mai Tsarki3 Gama ya sāke giggina masujadai waɗanda Hezekiya, tsohonsa, ya rurrushe. Ya kakkafa bagadai don Ba'al, ya kuma yi Ashtarot. Ya yi sujada ga dukan rundunar sama, ya bauta musu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20203 Ya sāke gina masujadan kan tudun da mahaifinsa Hezekiya ya rurrushe; ya tā da bagadan Ba’al, ya kuma gina ginshiƙan Ashera. Ya rusuna wa dukan rundunonin taurari, ya kuma yi musu sujada. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa'ad da aka gama duka, sai dukan Isra'ilawa da suka hallara, suka bi cikin biranen Yahuza, suka farfashe al'amudan, suka ragargaza Ashtarot, suka farfashe masujadai da bagadai duka da suke a Yahuza da Biliyaminu, da na Ifraimu da Manassa har suka hallakar da su duka. Sa'an nan dukan jama'ar Isra'ila suka koma garuruwansu, ko wanne zuwa mahallinsa.
Sa'an nan sarki Yosiya ya umarci Hilkiya, babban firist, da firistoci masu daraja ta biyu, da masu tsaron ƙofa, su fitar da tasoshin da aka yi wa Ba'al, da Ashtoret, da dukan taurarin sama, daga cikin Haikalin Ubangiji. Sai ya ƙone su a bayan Urushalima a saurar Kidron, sa'an nan ya kwashe tokarsu zuwa Betel.