2 Tarihi 32:8 - Littafi Mai Tsarki8 Hannun mutum yake tare da shi, amma mu Ubangiji Allahnmu yake tare da mu, domin ya taimake mu, ya yi yaƙi dominmu.” Mutane kuwa suka amince da maganar Hezekiya, Sarkin Yahuza. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20208 Mayaƙa na jiki ne kawai suke tare da shi, amma Ubangiji Allahnmu ne yake tare da mu, zai kuwa taimake mu yă kuma yi yaƙinmu.” Mutane kuwa suka amince da maganar Hezekiya, Sarkin Yahuda. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Asa kuwa ya yi kuka ga Ubangiji Allahnsa, ya ce, “Ya Ubangiji, ba wani mai taimako kamarka, wanda zai yi taimako sa'ad da mai ƙarfi zai kara da marar ƙarfi, ka taimake mu, ya Ubangiji Allahnmu, gama a gare ka muke dogara, da sunanka kuma muka zo don mu yi yaƙi da wannan babbar runduna. Ya Ubangiji, kai ne Allahnmu, kada ka bar mutum ya rinjayi jama'arka.”