Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Tarihi 32:19 - Littafi Mai Tsarki

19 Suka yi ta magana a kan Allah na Urushalima, kamar yadda suka yi magana a kan gumakan al'ummai, wato aikin hannuwan mutane.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 Suka yi magana game da Allah na Urushalima yadda suka yi game da allolin sauran mutanen duniya, aikin hannuwan mutane.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Tarihi 32:19
31 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ƙasarsu tana cike da gumaka, suna sujada ga abubuwan da suka yi da hannuwansu.


Sun jefar da gumakansu cikin wuta, gama su ba Allah ba ne, amma ayyukan hannuwan mutane ne, waɗanda aka yi da itace da dutse, saboda haka an iya a hallaka su.


Amma ku kun iso Ɗutsen Sihiyona ne, da birnin Allah Rayayye, Urushalima ta Sama, wurin dubban mala'iku.


Gama jama'ar Isra'ila da ta Yahuza, tun daga ƙuruciyarsu, ba su aikata kome a gabana ba sai mugunta, ba abin da jama'ar Isra'ila suka yi, sai tsokanata da gumaka don in yi fushi da ayyukan hannuwansu, ni Ubangiji na faɗa.


An kawo fallayen azurfa daga Tarshish, Da zinariya kuma daga Ufaz, Aikin gwanaye da maƙeran zinariya. Tufafinsu na mulufi ne da shunayya, duka aikin gwanaye.


Gama al'adun mutane na ƙarya ne, Daga cikin jeji aka sare wani itace, Gwanin sassaƙa ya sassaƙa shi da gizago.


Zan hurta hukuncin da zan yi musu saboda dukan muguntarsu, da suka bar bina, suka ƙona turare ga gumaka, suka kuma bauta wa gumakan da suka yi.


suka ƙaƙƙone gumakansu waɗanda ba Allah ba ne ko kaɗan, siffofi ne kurum na itace da na dutse, da mutane suka yi da hannuwansu.


Ƙaƙa za mu amsa wa manzannin da suka zo gare mu daga Filistiya? Za mu faɗa musu, cewa Ubangiji ya tabbatar da Sihiyona, jama'arsa da suke shan wahala kuwa za su sami zaman lafiya a can.


A maimakonsu sai ya zaɓi kabilar Yahuza. Ya zaɓi Dutsen Sihiyona, wanda yake ƙauna ƙwarai.


Amma na zaɓi Urushalima domin sunana ya kasance a wurin, na kuma zaɓi Dawuda ya zama shugaban jama'ata Isra'ila.’


Baranka ya taɓa kashe zaki da beyar, wannan arne zai zama kamar ɗaya daga cikinsu, tun da yake ya raina rundunar Allah mai rai.


“ ‘La'ananne ne mutumin da ya sassaƙa, ko ya ƙera gumaka, abar ƙyama ce ga Ubangiji, aikin hannun mai sana'a, ya kafa ta a ɓoye.’ “Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’


Can za ku bauta wa gumaka na itace, da na duwatsu, aikin hannuwan mutum, waɗanda ba su gani, ko ji, ko ci, ko sansana.


Sai sarki Hezekiya, da annabi Ishaya ɗan Amoz, suka yi addu'a saboda wannan al'amari, suka yi kuka zuwa Sama.


Annabin Allah kuwa ya je wurin Sarkin Isra'ila ya ce masa, “Ubangiji ya ce, ‘Tun da yake Suriyawa sun ce, Ubangiji shi Allah na tuddai ne, ba Allah na kwari ba, saboda haka zan ba da dukan wannan taron jama'a a hannunka, za ka sani ni ne Ubangiji.’ ”


Amma ka tuna fa, ya Ubangiji, abokan gābanka suna yi maka ba'a, Su wawaye ne waɗanda suke raina ka.


Ubangiji Allah ya ce, “Da yake Mowab da Seyir sun ce mutanen Yahuza sun zama kamar al'ummai,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ