7 A wata na uku ne suka fara tattara tsibi tsibin, suka gama a wata na bakwai.
7 Sun fara yin haka a wata na uku, suka kuma gama a wata na bakwai.
Jama'ar Isra'ila da na Yahuza waɗanda suke zaune a garuruwan Yahuza, su ma sun kawo tasu zaka ta shanu, da ta tumaki, da ta abubuwan da aka keɓe aka kuma tsarkake domin Ubangiji Allahnsu, suka tara su tsibi tsibi.
Sa'ad da Hezekiya da sarakuna suka zo suka ga tsibi tsibin, sai suka yabi Ubangiji da jama'arsa Isra'ila.