Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Tarihi 30:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Sai suka ba da umarni a yi shela a Isra'ila duka, tun daga Biyer-sheba, har zuwa Dan, cewa sai mutane su zo Idin Ƙetarewa na Ubangiji Allah na Isra'ila a Urushalima, gama jama'a mai yawan gaske ba su zo wurin yin idin kamar yadda aka umarta ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Suka yanke shawara su yi shelar a ko’ina a Isra’ila, daga Beyersheba zuwa Dan, suna kiran mutane su zo Urushalima, suka kuma yi Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji Allah na Isra’ila. Ba a yi bikin da mutane masu yawa bisa ga abin da aka rubuta ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Tarihi 30:5
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Dukan jama'ar Isra'ila fa suka fito tun daga Dan a arewa har zuwa Biyer-sheba a kudu da kuma Gileyad daga gabas. Suka hallara gaba ɗaya a gaban Ubangiji a Mizfa.


Ina yaba muku ne don kuna tunawa da ni a cikin kowace harka, kuna kuma riƙe ka'idodin nan da kyau, daidai yadda na ba ku.


Yanzu, ya sarki, sai ka tabbatar da dokar, ka sa hannu, don kada a sāke ta, gama dokar Mediya da Farisa ba a soke ta.”


Ubangiji kuwa ya iza Sairus Sarkin Farisa a shekarar da ya ci sarauta, domin a cika maganar da Ubangiji ya faɗa wa Irmiya. Sai ya yi shela a dukan ƙasar mulkinsa, aka kuma rubuta shelar.


Ba a taɓa yin Idin Ƙetarewa irin wannan ba tun kwanakin annabi Sama'ila, ba wani kuma daga cikin sarakunan Isra'ila da ya kiyaye Idin Ƙetarewa kamar yadda Yosiya ya kiyaye shi tare da firistoci, da Lawiyawa, da dukan mutanen Yahuza da na Isra'ila, waɗanda suke a wurin, da kuma mazaunan Urushalima.


Sai aka yi shela a Yahuza da Urushalima, a kawo wa Ubangiji kuɗin da Musa, bawan Allah, ya aza wa Isra'ila sa'ad da suke cikin jeji.


“Ku lura, ku aikata dukan abin da na umarce ku da shi, kada ku ƙara, kada ku rage daga cikinsa.


Su yi waɗannan idodi a ƙayyadaddun lokatai.


waɗannan ka'idodi domin ƙayyadaddun idodi sa'a da Isra'ilawa za su taru domin yin sujada.


Ibrahim ya tashi da sassafe, ya kuma ɗauki gurasa da salkar ruwa, ya bai wa Hajaratu, ya ɗora kafaɗarta. Sai ya ba ta ɗanta, ya sallame ta. Ta tafi ta yi ta yawo cikin jejin Biyer-sheba.


A ganin sarki da na jama'a duka, shirin ya yi daidai.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ