4 A ganin sarki da na jama'a duka, shirin ya yi daidai.
4 Shirin ya yi kyau ga sarki da kuma dukan taron.
Jama'a kuwa suka amince da shawarar, suka yarda kuma a yi haka ɗin.
gama ba su iya yinsa a lokacinsa ba, saboda yawan firistocin da suka tsarkake kansu bai isa ba, mutane kuma ba su taru a Urushalima ba.
Sai suka ba da umarni a yi shela a Isra'ila duka, tun daga Biyer-sheba, har zuwa Dan, cewa sai mutane su zo Idin Ƙetarewa na Ubangiji Allah na Isra'ila a Urushalima, gama jama'a mai yawan gaske ba su zo wurin yin idin kamar yadda aka umarta ba.