Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Tarihi 30:23 - Littafi Mai Tsarki

23 Sai dukan taron suka yarda su ci gaba da yin idin har waɗansu kwana bakwai ɗin kuma, sai suka ci gaba da yin idin har kwana bakwai da murna.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

23 Dukan mutanen suka yarda su ƙara kwana bakwai kuma, sai suka ci gaba da bikin cikin farin ciki har waɗansu kwana bakwai kuma.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Tarihi 30:23
5 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sa'an nan kuma Sulemanu ya yi biki na kwana bakwai, shi da dukan jama'ar Isra'ila. Mutane suka zo, tun daga Mashigin Hamat a arewa, har zuwa iyakar ƙasar Masar a kudu, suka hallara a gaban Ubangiji Allahnmu.


A rana ta takwas kuwa suka yi wani muhimmin taro, domin su keɓe bagaden. Sun yi kwana bakwai suna yin bikin.


Gama Hezekiya, Sarkin Yahuza, ya ba taron bijimai dubu (1,000) da tumaki dubu bakwai (7,000), don yin hadayu, sarakuna kuma sun ba taron bijimai dubu (1,000) da tumaki dubu goma (10,000). Firistoci da yawa suka tsarkake kansu.


Sai sarki Hezekiya tare da sarakunansa, suka faɗa wa Lawiyawa su yi ta raira yabo ga Ubangiji da kalmomin Dawuda, da na Asaf maigani. Da murna suka raira yabo, suka sunkuya suka yi sujada.


Dukan taron jama'ar da suka komo daga zaman talala suka yi wa kansu bakkoki, suka zauna cikinsu, gama tun daga kwanakin Joshuwa ɗan Nun, har zuwa wannan rana, jama'ar Isra'ila ba su yin haka. Aka kuwa yi farin ciki mai yawa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ