A shekara ta arbaminya da tamanin bayan fitowar mutanen Isra'ila daga ƙasar Masar, a shekara ta huɗu ta sarautar Sulemanu, Sarkin Isra'ila, a watan biyu, wato watan Zib, sai Sulemanu ya fara gina Haikalin Ubangiji.
Sulemanu kuwa ya fara ginin Haikalin Ubangiji a Urushalima a kan Dutsen Moriya, inda Ubangiji ya taɓa bayyana ga tsohonsa Dawuda, inda kuma Dawuda ya riga ya shirya a daidai masussukar Arauna Bayebuse.