Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Tarihi 26:21 - Littafi Mai Tsarki

21 Ta haka sarki Azariya ya kuturce, har zuwa ranar mutuwarsa. Saboda kuturtarsa, ya zauna a keɓe a wani gida, gama an fisshe shi daga Haikalin Ubangiji. Yotam ɗansa shi ya shugabanci iyalin gidan sarki, yana kuma mulkin jama'ar ƙasa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

21 Sarki Uzziya ya kasance da kuturta har ranar mutuwarsa. Ya zauna a gidan da aka ware, da kuturci, aka kuma ware shi daga haikalin Ubangiji. Yotam ɗansa ya lura da fadan ya kuma yi mulkin mutanen ƙasar.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Tarihi 26:21
9 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Muddin yana da cutar, zai zama marar tsarki. Zai zauna shi kaɗai a bayan zango.


Akwai mutum huɗu, kutare, waɗanda suke zaune a bakin ƙofar gari, sai suka ce wa junansu, “Me ya sa muke zaune nan har mu mutu?


Aka fitar da Maryamu a bayan zangon har kwana bakwai. Jama'ar kuwa ba su ci gaba da tafiya ba, sai da aka shigar da Maryamu a zangon.


Shi kuwa wanda za a tsarkake, sai ya wanke tufafinsa, ya aske dukan gashinsa, ya yi wanka da ruwa, zai kuwa tsarkaka. Bayan wannan zai shiga zango, amma kada ya shiga cikin alfarwarsa har kwana bakwai.


Sai Azariya babban firist tare da sauran firistocin suka dube shi, sai ga kuturta a goshinsa! Sai suka tunkuɗa shi waje nan da nan. Shi kansa ma ya hazarta ya fita saboda Ubangiji ya buge shi.


Sai Isra'ilawa suka fitar da su daga cikin zango kamar yadda Ubangiji ya faɗa wa Musa. Haka mutanen Isra'ila suka yi.


Yotam yana da shekara ashirin da biyar sa'ad da ya ci sarauta, ya kuwa yi mulki shekara goma sha shida a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Yerusha 'yar Zadok.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ