Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Tarihi 26:19 - Littafi Mai Tsarki

19 Azariya ya yi fushi, a lokacin kuwa yana riƙe da farantin ƙona turare a hannunsa, sa'ad da ya yi fushi da firistocin, sai kuturta ta faso a goshinsa, a nan gaban firistocin a cikin Haikalin Ubangiji, wajen bagaden ƙona turare.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 Uzziya wanda yake da farantin wuta a hannunsa a shirye don ƙone turare, ya husata. Yayinda yake fushi da firistocin a gabansu a gaban bagaden turare a haikalin Ubangiji, sai kuturta ta faso a goshinsa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Tarihi 26:19
7 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sa'ad da al'amudin girgijen ya tashi daga kan alfarwar, sai ga Maryamu ta kuturce, fari fat kamar auduga. Da Haruna ya juya wajen Maryamu, ya ga ta zama kuturwa.


Yana magana ke nan, sai sarki ya ce masa, “Yaushe muka naɗa ka mai ba sarki shawara? Ka rufe baki! In kuwa ba haka ba in sa a kashe ka.” Sai annabin ya yi shiru, amma ya ce, “Na dai sani Allah ya riga ya shirya zai hallaka ka, saboda ka aikata wannan, ba ka kuma saurari shawarata ba.”


Sai Asa ya yi fushi da maiganin, ya sa shi a kurkuku saboda maganar da ya yi masa, gama ya husata da shi ƙwarai. A wannan lokaci kuma sai Asa ya ƙuntata wa waɗansu daga cikin jama'a.


Firist kuwa ya dudduba shi, in akwai kumburi a fatar jikin mutum wanda ya rikiɗar da gashin wurin ya zama fari, in kuma akwai sabon miki a kumburin,


Da sarki ya komo daga Dimashƙu, ya hango bagaden, sai ya tafi kusa da shi.


Sai Azariya babban firist tare da sauran firistocin suka dube shi, sai ga kuturta a goshinsa! Sai suka tunkuɗa shi waje nan da nan. Shi kansa ma ya hazarta ya fita saboda Ubangiji ya buge shi.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ