2 Tarihi 26:15 - Littafi Mai Tsarki15 A Urushalima ya yi na'urori waɗanda gwanayen mutane ne suka ƙago don a sa su a hasumiya, da kan kusurwoyi, don a harba kibau, da manyan duwatsu. Da haka sunansa ya bazu ko'ina, gama ya sami taimako mai banmamaki, har ya zama mai ƙarfin gaske. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202015 A Urushalima ya yi na’urori da gwanaye suka sarrafa don amfani a hasumiyoyi da kuma a kusurwar kāriya don harbin kibiyoyi da jefan manyan duwatsu. Sunansa ya bazu ko’ina, gama ya sami taimako sosai har ya zama mai iko. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Shi ɗan wata mace mutuniyar Dan, mahaifinsa kuwa mutumin Taya ne. Huram ya gwanance a kan aiki da zinariya, da azurfa, da tagulla, da baƙin ƙarfe, da dutse, da itace, da kuma shuɗi, da shunayya, da garura, da lilin mai kyau. Shi kuma zai iya sassaƙa kowane irin abu da aka sa shi ya sassaƙa, tare da gwanayenka, da na tsohonka, ubangidana, wato Dawuda.
Saboda haka sai ka aiko mini da mutum wanda ya gwanance a kan aiki da azurfa, da tagulla, da baƙin ƙarfe, da kuma shunayya, da garura, da shuɗɗan zare, da wanda kuma ya gwanance da aikin sassaƙa, domin ya yi aiki tare da gwanayen mutane da nake da su a Yahuza da Urushalima, waɗanda tsohona Dawuda ya kawo.