Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Tarihi 26:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Dukan jama'ar Yahuza fa suka ɗauki Azariya, ɗan shekara goma sha shida, suka naɗa shi sarki, ya gāji gadon sarautar tsohonsa Amaziya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Sai dukan mutanen Yahuda suka ɗauki Uzziya wanda yake da shekara goma sha shida da haihuwa, suka naɗa shi sarki a madadin mahaifinsa Amaziya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Tarihi 26:1
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai mazaunan Urushalima suka naɗa Ahaziya, autansa, ya gāji gadon sarauta, saboda ƙungiyar mutanen da suka zo tare da Larabawa a sansanin sun karkashe dukan 'yan'uwansa maza. Ahaziya ɗan Yoram Sarkin Yahuza, ya fara mulki.


Jama'ar ƙasar kuwa suka karkashe dukan waɗanda suka yi wa sarki Amon maƙarƙashiyar, suka naɗa Yosiya, ɗansa, ya gāji gadon sarautarsa.


Sai dukan mutanen Yahuza suka ɗauki Azariya mai shekara goma sha shida, suka sarautar da shi don ya gāji tsohonsa Amaziya.


Sai suka kawo shi a bisa dawakai, suka binne shi tare da kakanninsa a birnin Dawuda.


Ya gina Elat, ya komar da ita ga Yahuza, bayan rasuwar sarki.


Abin da yake rubuce a littafin nan, jawabi ne a kan Yahuza da Urushalima, wanda Allah ya bayyana wa Ishaya ɗan Amoz a zamanin da Azariya, da Yotam, da Ahaz, da Hezekiya, suka yi sarautar Yahuza.


Ubangiji kuwa ya yi magana da Yusha'u ɗan Beyeri a zamanin mulkin Azariya, da Yotam, da Ahaz, da Hezekiya, sarakunan Yahuza, da zamanin mulkin Yerobowam ɗan Yehowash, Sarkin Isra'ila.


Ga zantuttukan Amos, ɗaya daga cikin makiyayan ƙauyen Tekowa. Allah ya bayyana wa Amos wannan saƙo, tun shekara biyu kafin girgizar duniya, a lokacin da Azariya yake sarautar Yahuza, Yerobowam ɗan Yehowash kuwa yake sarautar Isra'ila.


A shekara ta biyu ta sarautar Yehowash ɗan Yehowahaz Sarkin Isra'ila, Amaziya ɗan Yowash Sarkin Yahuza ya ci sarauta.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ