Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Tarihi 25:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Sa'an nan Amaziya ya tattara mazajen Yahuza, ya kasa su bisa ga gidajen kakanninsu, a ƙarƙashin shugabanni na dubu dubu, da na ɗari ɗari, a dukan Yahuza da Biliyaminu. Sai ya tara 'yan shekara ashirin ko fi, ya sami mutum dubu ɗari uku (300,000) ƙarfafa, waɗanda suka isa zuwa yaƙi, wato za su iya riƙon māshi da garkuwa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Amaziya ya tattara mutanen Yahuda ya kuma ba su aiki bisa ga iyalansu, ya ba da aiki ga shugabannin dubu-dubu da shugabannin ɗari-ɗari, a dukan Yahuda da Benyamin. Ya kuma tattara waɗanda suke ’yan shekara ashirin da haihuwa ko fiye ya sami mutane dubu ɗari uku da suke a shirye don aikin soja, da suka isa riƙe māshi da garkuwa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Tarihi 25:5
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

daga mai shekara ashirin zuwa sama waɗanda suka isa zuwa yaƙi.


Sa'ad da Rehobowam ya kai Urushalima, sai ya tattara zaɓaɓɓun mayaƙa, mutum dubu ɗari da dubu tamanin (180,000) daga cikin jama'ar Yahuza da ta Biliyaminu don su yi yaƙi da Isra'ila, su komo wa Rehobowam da mulki.


Suna da sojoji dubu ɗari uku da dubu bakwai da ɗari biyar (307,500) a ƙarƙashin ikonsu waɗanda suke da ƙarfin yin yaƙi sosai, da za su taimaki sarki a kan maƙiyansa.


Sarki Asa kuwa yana da soja dubu ɗari uku (300,000) a Yahuza, ko wanne yana da kutufani da māshi, yana da soja dubu ɗari biyu da dubu tamanin (280,000) daga Biliyaminu, 'yan baka ko wanne da garkuwarsa. Dukansu manyan jarumawa ne.


Ga lissafin kawunan iyalin Isra'ilawa, da shugabannin dangi, da jama'a masu gudanar da ayyukan mulki. A kowane wata akan sauya aikin ƙungiyar mutum dubu ashirin da dubu huɗu (24,000), a ƙarƙashin shugaban aiki na wannan wata. Kowane wata akan sauya, wata ƙungiya ta kama aiki.


Sa'an nan Dawuda ya yi shawara da shugabannin sojoji na dubu dubu da na ɗari ɗari, da kowane shugaba.


Waɗansu kuma zai sa su zama shugabannin mutum dubu dubu da na hamsin hamsin. 'Ya'yanku ne za su riƙa yi masa noma da girbi, su ƙera masa kayayyakin yaƙi da na karusansa.


Sai Musa ya zaɓi isassun mutane daga cikin Isra'ilawa ya naɗa su shugabannin jama'a na dubu dubu, da na ɗari ɗari, da na hamsin hamsin, da na goma goma.


Ya kuma ɗauko sojan haya, mutum dubu ɗari (100,000) jarumawa daga Isra'ila a bakin talanti ɗari na azurfa.


Sai ya ce wa mutanen Yahuza, “Bari mu giggina waɗannan birane, mu kewaye su da garu, da hasumiya, da ƙofofi masu ƙyamare. Ƙasar tamu ce har yanzu, saboda mun nemi Ubangiji Allahnmu. Mun neme shi, ya kuwa ba mu salama a kowace fuska.” Suka yi ta gini, suka kuwa arzuta.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ