2 Tarihi 25:4 - Littafi Mai Tsarki4 Amma bai karkashe 'ya'yansu ba, bisa ga abin da yake a rubuce a Shari'a, wato Attaura ta Musa, inda Ubangiji ya yi umarni cewa, “Ba za a kashe iyaye saboda 'ya'yansu ba, ba za a kuma kashe 'ya'ya saboda iyaye ba, amma mutum zai mutu saboda laifin kansa.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20204 Duk da haka bai kashe ’ya’yansu maza ba amma ya yi bisa ga abin da yake a rubuce a cikin Doka, a cikin Littafin Musa, inda Ubangiji ya umarta, “Ba za a kashe iyaye saboda ’ya’yansu ba; ba kuwa za a kashe ’ya’ya saboda iyayensu ba; kowa zai mutu saboda zunubansa ne.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa'an nan Amaziya ya tattara mazajen Yahuza, ya kasa su bisa ga gidajen kakanninsu, a ƙarƙashin shugabanni na dubu dubu, da na ɗari ɗari, a dukan Yahuza da Biliyaminu. Sai ya tara 'yan shekara ashirin ko fi, ya sami mutum dubu ɗari uku (300,000) ƙarfafa, waɗanda suka isa zuwa yaƙi, wato za su iya riƙon māshi da garkuwa.