2 Tarihi 24:7 - Littafi Mai Tsarki7 Gama 'ya'ya maza na Ataliya, muguwar matan nan, sun kutsa kai a cikin Haikalin Ubangiji, suka yi amfani da dukan tsarkakan kayayyakin Haikalin Ubangiji domin gumaka. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20207 Yanzu ’ya’ya muguwar macen nan Ataliya maza sun fasa zuwa cikin haikalin Allah, suka kuma yi amfani da kayayyaki masu tsarki ma wa Ba’al. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Maimakon haka, sai ka nuna wa Ubangiji girmankai, har ka sa aka kawo maka, kai da fādawanka, da matanka, da ƙwaraƙwaranka, tasoshin Haikalin Ubangiji, kuka sha ruwan inabi a cikinsu. Kuka yabi gumakan zinariya da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse waɗanda ba su ji, ba su gani, ba su da ganewar kome. Amma ba ka girmama Allah ba, wanda ranka da dukan harkokinka suna a hannunsa.