Gama 'ya'ya maza na Ataliya, muguwar matan nan, sun kutsa kai a cikin Haikalin Ubangiji, suka yi amfani da dukan tsarkakan kayayyakin Haikalin Ubangiji domin gumaka.
Sai suka ƙyale Haikalin Ubangiji Allah na kakanninsu, suka bauta wa Ashtarot da gumaka. Hasala kuwa ta auko a kan Yahuza da Urushalima, saboda wannan mugunta da suka yi.