2 Tarihi 24:13 - Littafi Mai Tsarki13 Sai ma'aikatan da aka sa su yi aikin, suka yi aiki sosai, suka tafiyar da gyaran, suka gyara Haikalin Ubangiji, ƙarfinsa ya koma kamar yadda yake dā. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202013 Mutanen da suke lura da aikin natsattsu ne, kuma gyare-gyaren suka ci gaba a ƙarƙashinsu. Suka sāke gina haikalin Allah bisa ga ainihin fasalinsa suka ƙara masa ƙarfi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Da suka gama aikin, sai suka kawo wa sarki da Yehoyada sauran kuɗin. Da waɗannan kuɗin aka yi tasoshi, da kayan girke-girke na Haikalin Ubangiji, da kuma kayan hidima da miƙa hadayu na ƙonawa, da tasoshi domin turare, da kwanoni na zinariya da na azurfa. Suka yi ta miƙa hadayu na ƙonawa a cikin Haikalin Ubangiji, dukan kwanakin Yehoyada.