2 Tarihi 24:12 - Littafi Mai Tsarki12 Sarki kuwa da Yehoyada suka ba da kuɗin ga waɗanda suke lura da aikin Haikalin Ubangiji. Suka sa magina, da masassaƙa su gyara Haikalin Ubangiji, suka kuma sa masu aikin baƙin ƙarfe da na tagulla su gyara Haikalin Ubangiji. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202012 Sarki da Yehohiyada suka ba da shi ga mutanen da suka yi aikin da ake bukata don haikalin Ubangiji. Suka ɗauki masu gini da kafintoci don su gyara haikalin Ubangiji, da kuma ma’aikatan ƙarafa da tagulla don su gyara haikalin. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Duk lokacin da Lawiyawa suka kawo wa 'yan majalisar sarki babban akwatin sa'ad da suka gan shi cike da kuɗi, sai magatakardan sarki, da na'ibin babban firist, su zo su juye kuɗin da suke cikin babban akwatin, sa'an nan su mayar da shi a inda yake. Haka suka yi ta yi kullum, har suka tara kuɗi masu yawan gaske.