Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Tarihi 24:11 - Littafi Mai Tsarki

11 Duk lokacin da Lawiyawa suka kawo wa 'yan majalisar sarki babban akwatin sa'ad da suka gan shi cike da kuɗi, sai magatakardan sarki, da na'ibin babban firist, su zo su juye kuɗin da suke cikin babban akwatin, sa'an nan su mayar da shi a inda yake. Haka suka yi ta yi kullum, har suka tara kuɗi masu yawan gaske.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 Duk sa’ad da Lawiyawa suka fito da akwatin zuwa ga hafsoshin sarki, suka kuma ga cewa akwatin yana da kuɗi mai yawa, sai magatakardan fada da hafsan babban firist su zo su juya kuɗin daga akwatin su mai da shi wurinsa. Sun riƙa yin haka kullum suka tara kuɗi mai yawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Tarihi 24:11
4 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A kowace ranar farko ta mako, kowannenku ya riƙa tanada wani abu, yana ajiyewa gwargwadon samunsa, kada sai na zo tukuna, a tara gudunmawa.


Sai dukan sarakuna, da dukan jama'a, suka yi farin ciki, suka kawo kuɗin da aka aza musu, suka zuba a babban akwatin, har ya cika.


Sarki kuwa da Yehoyada suka ba da kuɗin ga waɗanda suke lura da aikin Haikalin Ubangiji. Suka sa magina, da masassaƙa su gyara Haikalin Ubangiji, suka kuma sa masu aikin baƙin ƙarfe da na tagulla su gyara Haikalin Ubangiji.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ