2 Tarihi 23:18 - Littafi Mai Tsarki18 Yehoyada kuma ya sa matsaran da za su yi tsaron Haikalin Ubangiji a ƙarƙashin ikon firistoci, Lawiyawa, waɗanda Dawuda ya shirya don su lura da Haikalin Ubangiji, su miƙa hadayu na ƙonawa ga Ubangiji, yadda aka rubuta a Attaura ta Musa, da murna da waƙa kamar yadda Dawuda ya shirya. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202018 Sa’an nan Yehohiyada ya sa aikin lura da haikalin Ubangiji a hannuwan firistoci, waɗanda suke Lawiyawan da Dawuda ya ba su aikin haikali don su miƙa hadayun ƙonawa na Ubangiji kamar yadda yake a rubuce a Dokar Musa, da farin ciki da kuma rerawa, kamar yadda Dawuda ya umarta. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sai firistoci suka tsaya a matsayinsu, haka kuma Lawiyawa suka tsaya a nasu matsayi riƙe da kayansu na bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe, waɗanda sarki Dawuda ya yi domin yabon Ubangiji, gama madawwamiyar ƙaunarsa tabbatacciya ce har abada. A duk lokacin da Dawuda zai yabi Ubangiji tare da su, sai firistoci waɗanda suke daura da su su busa ƙaho, sa'an nan sai dukan Isra'ilawa su miƙe tsaye.