Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Tarihi 23:16 - Littafi Mai Tsarki

16 Sai Yehoyada da dukan jama'a, da sarkin, suka ɗauki alkawari za su zama jama'ar Ubangiji.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 Sa’an nan Yehohiyada ya yi alkawari cewa shi da mutane da kuma sarki za su zama mutanen Ubangiji.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Tarihi 23:16
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Saboda wannan duka muke yin alkawari mai ƙarfi a rubuce. Shugabanninmu kuwa, da Lawiyawanmu, da firistocinmu, suka buga hatimi, suka sa hannu.”


“Yanzu na yi niyya a zuciyata in yi alkawari da Ubangiji Allah na Isra'ila, domin ya huce daga zafin fushin da yake yi da mu.


Yehoyada kuwa ya yi alkawari tsakanin Ubangiji, da sarki, da jama'a, yadda za su zama jama'ar Ubangiji. Ya kuma yi alkawari tsakanin sarki da jama'a.


“Da ɗaya ɗaya da ɗaya ɗaya mutane za su ce, ‘Ni na Ubangiji ne!’ Za su zo su haɗa kai da jama'ar Isra'ila. Ko wanne zai ɗaura sunan Ubangiji a dantsensa, Ya ce da kansa ɗaya daga cikin mutanen Allah.”


Bari mu yi alkawari da Allahnmu, mu kori dukan waɗannan mata da 'ya'yansu, bisa ga shawarar shugabanni da waɗanda suke rawar jiki saboda umarnin Allah. Bari mu yi alkawari bisa ga doka.


Sai suka rantse wa Ubangiji da murya mai ƙarfi, suna sowa, suna busa kakaki da ƙaho.


Sai suka ƙulla alkawari, cewa za su nemi Ubangiji Allah na kakanninsu da dukan zuciyarsu da ransu.


Dukan Yahuza ta yi murna saboda rantsuwar, gama da zuciya ɗaya suka rantse, suka kuwa neme shi da iyakar aniya, sun kuwa same shi. Don haka Allah ya hutasshe su a kowane al'amari.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ