2 Tarihi 23:13 - Littafi Mai Tsarki13 Sa'ad da ta duba, sai ga sarki yana tsaye wajen ginshiƙin bakin ƙofa, ga shugabanni da masu busa ƙaho kewaye da sarkin. Dukan jama'a suna murna, suna busa ƙaho, mawaƙa kuma da kayan kaɗe-kaɗe da na bushe-bushensu, suna shugabancin shagalin. Sai Ataliya ta yayyage tufafinta ta ce, “Tawaye! Tawaye!” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202013 Ta duba, a can kuwa ga sarki, tsaye kusa da ginshiƙinsa a mashigi. Manyan sojoji da masu bushe-bushe suna kusa da sarki, dukan mutanen ƙasar kuwa suna farin ciki suna busa ƙahoni, mawaƙa kuma da kayan kiɗi suna bi da yabo. Sai Ataliya ta yage rigunanta ta yi ihu tana cewa, “Cin amanar ƙasa! Cin amanar ƙasa!” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Waɗanda kuma suke kusa da su har zuwa Issaka, da Zabaluna da Naftali, sun kawo abinci a kan jakuna, da raƙuma, da alfadarai, da takarkarai. Suka kawo abinci mai yawa, wato gāri da kauɗar ɓaure da nonnan busassun 'ya'yan inabi, da ruwan inabi, da man zaitun. Suka kuma kawo shanu da tumaki domin yanka a ci. Duk an yi wannan domin a nuna farin ciki ƙwarai a cikin dukan ƙasar Isra'ila.