Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Tarihi 22:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Ya kuma sa aka nemi Ahaziya. Aka kamo shi sa'ad da ya ɓuya a Samariya, suka kawo shi wurin Yehu, suka kashe shi, suka binne shi, gama suka ce, “Shi jikan Yehoshafat ne wanda ya nemi Ubangiji da zuciya ɗaya.” Don haka a gidan Ahaziya ba wanda ya isa ya riƙe mulkin.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Ya kuma sa aka nemi Ahaziya. Aka kamo shi sa’ad da ya ɓuya a Samariya, suka kawo shi wurin Yehu, suka kashe shi, suka binne shi, gama sun ce, “Shi jikan Yehoshafat ne, wanda ya nemi Ubangiji da dukan zuciyarsa.” Ta haka babu wani a gidan Ahaziya da yake da ƙarfin cin gaba da mulkin.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Tarihi 22:9
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sa'ad da Yehu yake hukunta wa gidan Ahab, sai ya gamu da sarakunan Yahuza, da 'ya'yan 'yan'uwan Ahaziya, maza, suna yi wa Ahaziya hidima, sai ya karkashe su.


Yana da shekara talatin da biyu, ya ci sarauta, ya yi shekara takwas yana mulki a Urushalima, ba wanda ya yi baƙin cikin mutuwarsa. Aka binne shi a birnin Dawuda, amma ba a kaburburan sarakuna ba.


Suka zo suka faɗa wa Yahuza da yaƙi. Suka washe dukan dukiyar da aka samu a gidan sarki, suka tafi da ita. Suka kuma kwashe 'ya'yansa, da matansa, ba wanda aka bar masa, sai Ahaziya autansa.


Sa'ad da Yoram ya hau gadon sarautar tsohonsa, ya kahu sosai, sai ya karkashe dukan 'yan'uwansa da takobi, ya kuma karkashe waɗansu daga cikin sarakunan Yahuza.


Dukan jama'ar Isra'ila za su yi makoki dominsa, su binne shi, gama shi kaɗai zai sami binnewa daga cikin gidan Yerobowam, domin a gare shi kaɗai aka iske abin da Ubangiji, Allah na Isra'ila, yake murna da shi.


sai ya kira annabin Allah, wanda ya zo daga Yahuza, ya ce, “Ubangiji ya ce, ‘Da yake ba ka yi biyayya da maganar Ubangiji ba, ba ka kuma kiyaye umarnin da Ubangiji Allahnka ya umarce ka da shi ba,


Sa'an nan Yehu ya shiga gida, ya ci ya sha, ya ce, “Ku san yadda za ku yi da wannan la'ananniyar mace, ku binne ta, gama ita 'yar sarki ce.”


Za ku neme ni ku same ni, idan kun neme ni da zuciya ɗaya.


Duk da haka an sami wani abin kirki a wurinka, gama ka kawar da gumakan Ashtarot daga ƙasar, ka sa zuciyarka ga neman Allah.”


Sa'ad da suka tafi, sun bar shi da rauni mai tsanani ƙwarai, sai barorinsa suka yi masa maƙarƙashiya suka kashe shi a gadonsa, saboda ya kashe ɗan Yehoyada firist. Ya mutu, aka binne shi a birnin Dawuda, amma ba su binne shi a kabarin sarakuna ba.


Daga lokacin da Amaziya ya bar bin Ubangiji, sai suka shirya masa maƙarƙashiya a Urushalima, amma ya gudu zuwa Lakish, sai suka sa a bi shi zuwa Lakish, a can suka kashe shi.


Sai fadawansa suka yi masa maƙarƙashiya, suka kashe shi a gidansa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ