Yehoram Sarkin Isra'ila ya tafi tare da Sarkin Yahuza da Sarkin Edom. Da suka yi kwana bakwai suna ta zagawa, sai sojoji da dabbobi suka rasa ruwan sha.
Sai Yoram ya wuce, shi da shugabannin sojojinsa tare da dukan karusansa. Sai ya tashi da dare ya fatattaki Edomawa waɗanda suka kewaye shi, shi da shugabannin karusansa.