2 Tarihi 20:26 - Littafi Mai Tsarki26 Sai suka taru a kwarin Beraka, wato albarka, a rana ta huɗu, a nan suka yabi Ubangiji. Don haka har wa yau ake kiran wurin, “Kwarin Beraka.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202026 A rana ta huɗu sai suka taru a Kwarin Beraka, inda suka yabi Ubangiji. Wannan ne ya sa ake kiransa Kwarin Beraka har wa yau. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Waɗannan su ne shugabannin sojoji, Ahiyezer, da Yowash, 'ya'yan Shemaiya, maza, daga Gibeya Yeziyel, da Felet, 'ya'yan Azmawet, maza Beraka, da Yehu daga Anatot Ismaya daga Gibeyon babban jarumi ne a cikin jarumawan nan talatin, yana daga cikin shugabannin jarumawa talatin ɗin Irmiya, da Yahaziyel Yohenan, da Yozabad daga Gedera Eluzai, da Yerimot, da Be'aliya Shemariya, da Shefatiya daga Harif Elkana, da Isshiya, da Azarel Yowezer, da Yashobeyam daga iyalin Kora Yowela, da Zabadiya 'ya'ya maza na Yeroham na Gedor.