Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Tarihi 20:23 - Littafi Mai Tsarki

23 Gama mutanen Ammon da na Mowab suka tasar wa mazaunan Dutsen Seyir, suka hallaka su ƙaƙaf. Sa'ad da suka karkashe mazaunan Seyir sai suka fāɗa wa juna, suka yi ta hallaka kansu da kansu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

23 Mutanen Ammon da Mowab suka tasar wa mazaunan Dutsen Seyir, suka hallaka su ƙaƙaf. Sa’ad da suka karkashe mazaunan Seyir sai suka fāɗa wa juna, suka yi ta hallaka juna.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Tarihi 20:23
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sa'an nan Saul da mutanen da suke tare da shi suka taru, suka tafi su yi yaƙi. Sai suka tarar Filistiyawa sun ruɗe suna ta yaƙi da junansu. Aka yi babbar yamutsewa.


Da suka busa ƙahonin nan ɗari uku, sai Ubangiji ya sa Madayanawa suka yi ta sassare junansu da takuba. Suka gudu zuwa Zerera har Bet-shitta, har kuma zuwa garin Abel-mehola, kusa da Tabbat.


Ishaku kuma na ba shi Yakubu da Isuwa. Na kuma ba Isuwa ƙasar tuddai ta Seyir, ya mallake ta, amma Yakubu da 'ya'yansa suka gangara zuwa Masar.


kada ku tsokane su, gama ko wurin sa ƙafa a ƙasarsu ba zan ba ku ba, gama na riga na ba Isuwa ƙasar tuddai ta Seyir.


da kuma Horiyawa cikin dutsen nan nasu, wato Seyir, har zuwa Elfaran a bakin jeji.


Da mutanen Yahuza suka zo hasumiyar tsaro ta jeji, suka duba sai suka ga gawawwaki kawai a kwance, ba wanda ya tsira.


A zamaninsa Edomawa suka tayar wa Yahuza, suka naɗa wa kansu sarki.


Ubangiji ya ce, “Zan ta da hargitsi a yi yaƙin basasa a Masar, ɗan'uwa ya yi gāba da ɗan'uwa, maƙwabci kuma gaba da maƙwabci. Biranen da suke hamayya za su yi faɗa da juna, sarakunan da suke hamayya kuma za su yi faɗa saboda neman iko.


Zan razana Gog da kowace irin razana, ni Ubangiji Allah na faɗa. Mutanensa za su sassare junansu da takubansu.


Zan kuma hamɓare gadon sarautan daula, in kuma karya ƙarfin daular al'umman. Zan kuma hallaka karusai da mahayansu. Sojojin dawakai kuma za su kashe junansu da takuba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ