2 Tarihi 20:22 - Littafi Mai Tsarki22 Sa'ad da suka fara raira waƙa, suna yabo, sai Ubangiji ya sa wa mutanen Ammon, da na Mowab, da na Dutsen Seyir, 'yan kwanto, 'yan kwanton kuwa suka fatattake su. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202022 Da suka fara waƙa, suna kuma yabo, sai Ubangiji ya kai hari a kan mutanen Ammon da Mowab da Dutsen Seyir, waɗanda suka kawo hari a Yahuda, aka kuwa ci su da yaƙi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ya zama aikin mabusan ƙaho ne, da mawaƙa duka, su haɗa kai, har a ji su suna yabon Ubangiji, suna godiya, sa'ad da suka ɗaga waƙa daidai da muryar ƙaho da ta kuge, da dukan kayan bushe-bushe suka yi ta raira waƙa cewa, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji Gama shi nagari ne, Ƙaunarsa kuwa madawwamiya ce.” Gidan kuwa, wato Haikalin Ubangiji, ya cika da girgije,