2 Tarihi 20:1 - Littafi Mai Tsarki1 Bayan wannan sai mutanen Mowab, da mutanen Ammon, tare da waɗansu daga cikin Me'uniyawa, suka zo su yi yaƙi da Yehoshafat. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20201 Bayan wannan, Mowabawa da Ammonawa tare da waɗansu Meyunawa suka zo su yaƙi Yehoshafat. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Amariya, babban firist, shi ne zai shugabance ku a kan dukan al'amuran da suke na wajen Ubangiji. Zabadiya, ɗan Isma'ilu mai mulkin gidan Yahuza, shi ne shugabanku a kan dukan al'amuran da suke na wajen sarki. Lawiyawa kuwa su zama muhimman ma'aikatanku. Kada ku ji tsoro a cikin aikinku, Ubangiji kuwa ya kasance tare da masu gaskiya.”