Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Tarihi 2:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Amma wa ya isa ya gina masa Haikali, shi wanda sama da saman sammai ba su iya ɗaukarsa ba. Ni wane ne da zan gina masa Haikali, sai dai wurin da za a riƙa ƙona turare a gabansa?

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Amma wa zai iya gina haikali dominsa, shi wanda sammai, har ma da sama sammai, ba za su iya riƙe shi ba? To, wane ne ni da zan gina haikali dominsa, in ba dai wurin ƙona hadayu a gabansa ba?

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Tarihi 2:6
19 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ubangiji ya ce, “Sama kursiyina ce, duniya kuwa matashin sawuna ce. Daga nan wane irin gida za ku iya ginawa domina, wane irin wuri ne kuma zan zauna?


“Ashe kuwa Allah zai zauna tare da ɗan adam a duniya? Ga shi kuwa, sama da saman sammai ba su iya ɗaukarka ba, balle fa ɗakin da na gina.


“Amma ko Allah zai zauna a duniya? Ga shi, Saman sammai ba ta isa ta karɓe ka ba, balle wannan Haikali da na gina!


Yanzu sai ka ba ni hikima da sani yadda zan iya kai da kawowa a gaban wannan jama'a, gama wa zai iya mulkin wannan jama'a taka mai yawa haka?”


“Amma wane ni ko kuma jama'ata, da za mu iya kawo sadaka mai yawa haka? Gama dukan kome daga gare ka yake. Daga cikin abin da muka karɓa daga wurinka muka ba ka.


Sarki Dawuda ya tafi ya zauna a gaban Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji Allah, ko ni ko iyalina ba mu cancanci dukan abin da ka yi mana ba.


Amma Musa ya ce wa Allah, “Wane ni in tafi gaban Fir'auna in fito da Isra'ilawa daga cikin Masar?”


Ko da yake ni ne mafi ƙanƙantar tsarkaka duka, ni aka ba wannan alheri in yi wa al'ummai bishara a kan yalwar Almasihu marar ƙididdiguwa,


Ga na ƙarshe ɗin, ƙanshin nan warin mutuwa ne, mai kaiwa ga hallaka, ga na farkon kuwa, ƙanshin rai ne mai kaiwa ga rai. To, wa zai iya ɗaukar nauyin waɗannan abubuwa?


Amma tsarkakakkun abubuwan da suke wajibanku da hadayunku na wa'adi, su ne za ku ɗauka ku kai wurin da Ubangiji ya zaɓa.


amma sai a wurin nan ɗaya wanda Ubangiji zai zaɓa daga cikin kabilanku, nan za ku miƙa hadayunku na ƙonawa, nan ne kuma za ku yi dukan abin da na umarce ku.


sai ku kai dukan abin da na umarce ku ku kai, wato hadayu na ƙonawa, da sadakokinku, da zakarku, da hadayunku na ɗagawa, da hadayunku na wa'adi da kuka yi wa Ubangiji a wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa ya sa sunansa.


“Mutum ya iya ɓoye kansa a wani lungu Inda ba zan iya ganinsa ba?” In ji Ubangiji. “Ashe, ban cika sammai da duniya ba?


da yankan duwatsu masu tamani na jerawa, da sassaƙa itace, da kowane irin aikin fasaha.


Sarki Sulemanu kuwa ya aika a kawo Huram daga Taya, gwanin aikin tagulla ne.


Shi ɗan wata mata ne daga kabilar Naftali wadda mijinta ya rasu. Huram mutumin Taya ne, maƙerin tagulla. Yana da hikima, da fahimi, da fasaha na iya yin kowane irin aiki da tagulla. Ya kuwa amsa kiran sarki Sulemanu, ya zo ya yi masa dukan aikinsa.


Kana da ma'aikata jingim, su masu fasa duwatsu, da magina, da masassaƙa, da gwanayen masu sana'o'i iri dabam dabam, masu yawan gaske.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ