2 Tarihi 2:3 - Littafi Mai Tsarki3 Sulemanu fa ya aika wurin Hiram Sarkin Taya ya ce, “Yadda ka yi wa tsohona Dawuda, wato ka aiko masa da itatuwan al'ul domin ya gina gida inda zai zauna, ni ma ina so ka yi mini haka. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20203 Solomon ya aika wannan saƙo ga Hiram sarkin Taya. “Ka aika mini gumaguman al’ul kamar yadda ka yi wa mahaifina Dawuda sa’ad da ka aika masa al’ul don yă gina fada yă zauna a ciki. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Haka kuwa Sulemanu ya yi dukan kayayyakin nan da suke cikin Haikalin Allah, duk da zinariya tsantsa aka yi su. bagade na zinariya tebur don ajiye gurasar ajiyewa alkukai tare da fitilunsu na zinariya tsantsa, domin a kunna su a gaban Wuri Mafi Tsarki na ciki kamar yadda aka tsara furanni fitilu arautaki hantsuka daruna cokula farantan wuta ƙofofi na can ciki ƙofofi na waje.
Da suka gama aikin, sai suka kawo wa sarki da Yehoyada sauran kuɗin. Da waɗannan kuɗin aka yi tasoshi, da kayan girke-girke na Haikalin Ubangiji, da kuma kayan hidima da miƙa hadayu na ƙonawa, da tasoshi domin turare, da kwanoni na zinariya da na azurfa. Suka yi ta miƙa hadayu na ƙonawa a cikin Haikalin Ubangiji, dukan kwanakin Yehoyada.