2 Tarihi 2:13 - Littafi Mai Tsarki13 Yanzu zan aika maka da Huram mutum mai gwaninta, mai ganewa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202013 “Zan aika maka Huram-Abi, wani gwani wanda ya iya aiki, kuma mai hikima, အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Saboda haka sai ka aiko mini da mutum wanda ya gwanance a kan aiki da azurfa, da tagulla, da baƙin ƙarfe, da kuma shunayya, da garura, da shuɗɗan zare, da wanda kuma ya gwanance da aikin sassaƙa, domin ya yi aiki tare da gwanayen mutane da nake da su a Yahuza da Urushalima, waɗanda tsohona Dawuda ya kawo.
Shi ɗan wata mace mutuniyar Dan, mahaifinsa kuwa mutumin Taya ne. Huram ya gwanance a kan aiki da zinariya, da azurfa, da tagulla, da baƙin ƙarfe, da dutse, da itace, da kuma shuɗi, da shunayya, da garura, da lilin mai kyau. Shi kuma zai iya sassaƙa kowane irin abu da aka sa shi ya sassaƙa, tare da gwanayenka, da na tsohonka, ubangidana, wato Dawuda.